1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar Jakadan Amirka a Libya

Halimatu AbbasSeptember 12, 2012

Jakadan Amirka a Libiya ya mutu a cikin harin da aka kai akan ofishinsa da ke birnin Benghazi na kasar Libiya

This undated photo released by the U.S. State Department shows U.S. Ambassador to Libya J. Christopher Stevens in an official portrait. Libyan officials say the U.S. ambassador and three other Americans have been killed in an attack on the U.S. consulate in the eastern city of Benghazi by protesters angry over a film that ridiculed Islam's Prophet Muhammad. (Foto:U.S. State Department/AP/dapd).
Mord an Botschafter J. Christopher Stevens in LibyenHoto: AP

A kasar Libiya an fuskanci mutuwar jakadan Amirka da ma'aikatansa uku bayan da wasu gungu dauke da makamai suka kai hari akan ofishin jakandancinsa da ke abrinin Bengazi domin nuna rashin amincewa da gwada wani filim dake zaman cin mutunci ga musulunci.

Yayin wannan zanga-zangar ne dai Jakadan na Amirka J . Christopher Stevens ya gamu da ajalinsa. Su dai wadannan mutane sun kai hari akan ofishin jakadancin ne domin nuna rashin amincewa da wani filim wanda a cewar mujallar Wall Street wani Bayahude dan kasar Amirka ya sarrafa shi. A cikin wannan filim Bayahuden ya kira addinin muslunci tamkar wata sankara tare da bayyanar da Annabi Mahaman tsira da aminci su tabbatar a gare shi a matsayin mazinaci. Ga dai abin da da daya daga ciki masu zang zangar ke cewa:

"Annabinmu Annabi Mahama (tsira da aminci su tabbata a gareshi) ba Osaman Bin Laden Ba. Shi mutun ne amma ba kamar sauran mutane ba. Shi ne annanbinmu. Shine fiyayyen hallita. A don haka zamu dauki matakin dakatar da gwada wannan filim."

An kuma gudanar da zanga-zanga a Masar

Zanga- zanga a AlkahiraHoto: dapd

Ko kafin a tabbatar da mutuwar jakadan sai da sakatriyar harkokin wajen Amirka Hilary Clinton ta yi jawabi wanda a ciki ta sanar da mutuwar wani jam'iin Amirka tana mai nuna matukar alhininta game da wannan rashi. Abdelmonoen al-Horr, kakakin hukumar tsaro ta ma'aikatar cikin gidan Libya tun da farko ya nunar da cewa daga wata gona da ke kusa da ofishin jakandancin ne aka kaddamar da harin. Wadanda suka shedar wa idanunsu sun ce maharan sun kuma kekece tutar Amirka suka kwashi ganima daga cikin ginin ko kafin su cusa masa wuta a jiya Talata da ke zaman ranar bukin zagoyowar harin da aka kai wa Amirka a ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2001. Majalisar dokokin Libya ta yi Allah wadai da wannan hari da kakkausan harshe. Shi dai harin na Libya ya auku ne bayan da dubban mutane suka shiga zanga-zanga makamaciyar haka a kasar Masar suna kona tutar Amirka tare da maye gurbinta da bakar tuta ta slama mai dauke da kalmar shahada. Kusan mutane 3000 ne suka yi dafifi a gaban ginin ofishin jakadancin domin nuna rashin amincewa da filim din da aka sarrafa a Amirka. Ga kuma yadda wani dan zanga-zanga ya nuna bacin ransa:

"Kowa na da 'yancinsa a duniya amma ba banda mu Musulmi. Suna tauye mana hakkinmu da kuma 'yancinmu.

Kiristoci sun nuna zumunci

Kiristocin CopticHoto: picture-alliance/dpa

Kiristoci mabiya darikar Koptic a kasar Masar su kuma a nasu bangaren sun sanar da yin zaman dirshen domin nuna rashin amincewarsu da filim din. Hakazalika kungiyar matasan ta Maspero su kuma sun yi Allah wadai da duk wani mataki na rena duk wani addini da kuma haddasa rashin jituwa tsakanin al'uma masu addinai dabam-dabam. Shi dai filim din mai suna "Innocence of Muslims" wato rashin sanin Musulmi Sam Bacile mai shekaru 52 daga jihar Carlifornia shi ne ya jagoranci sarrafa shi. Shi dai Bacile a cikin hirar da mujallar Wall street ta yi da shi ya bayyanar da Musulunci a matsayin wata sankara. Ba'ada bayan haka a cikin filim din ya bayyanar da Annabi Mahaman( tsira da aminci su tabbata a gare shi) wanda ba ya maganar komai in banda yin kisa ga kananan yara. Pastror Terry Jones da ke jihar Florida da a wani lokaci can baya aka gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da matakinsa na kona Alkur'ani shine ke tallata wannan filim.

Za ku iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe