Mutuwar mutane 12 a hare-haren Pakistan
January 25, 2011Wasu tagwayen hare-haren ta'addaci da aka ƙaddamar a biranen Karachi da Lahore na Pakistan sun haddasa mutuwar mutane aƘalla 12, tare da jikata da wasu da dama. Wani ɗan ƙunar baƙin wake ne ya tayar da bama -bamainda ke jikinsa a kusa ga wata makarantar 'yan shi'a da ke birnin Lahore. Yayin da a karachi wani ɗan ƙunar baƙin waken ya kai wani hari da yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu ƙarin mutane huɗu.
Tuni dai 'yan taliban suka ɗauki alhakin kai harin birnin Lahore wanda suka danganta shi da mayar da martani ga farmakin da sojojin ƙasar Pakistan ke kai musu, da kuma hare haren da jiragen yaƙin Amirka ke kai musu a wani yankin ƙasar da ke hannun yan Taliban. A ɗaya hannu kuma wani ɗan ƙunar baƙin waken da ke ɗauke ya tarwatsa jakkar da ke shaƙe da bama bamai a inda 'yan sanda biyu da kuma faran hula ɗaya suka mutu.
Mawallafi: Harouna Mamane/Mouhamadou Awal
Edita: Ahmed Tijjani Lawal