Mutuwar mutane 150 a rikicn tawayen Sudan
February 28, 2012
'Yan tawayen sudan sun bayyana cewar sun kashe dakarun gwamnati 150 a lokacin wani fito na fito da ya gudana tsakaninsu akan iyakar ƙasarsu da sudan ta kudu. Sai dai fadar mulki ta Khartoum ta ce akwai ƙarin gishiri a cikin labarin, ta na mai bayyana cewar sojojinta ne suka yi nasarar halaka 'yan tawaye da ta ce suna samun ɗaurin gindi da makobciyar ƙasa wato sudan ta kudu.
Ƙungiyar 'yan tawaye ta SPLM ta bayyana cewa tun a ranar lahadi ne ta kai harin haɗin guywa da takwararta ta Jem a Jau, wato wani yanki mai arzikin man fetur da kan iyaka. wannan dai shi ne karon farko da ƙungiyoyin 'yan tawayen biyu suka haɗa karfi domin yaƙar gwamnatin sudan. Sai dai hukumomin khartum suka ce sojojin kudancin sudan ne suka taimaka wa 'yan tawayen afka musu da faɗa. Lamarin a cewarsu ya saɓawa yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da aka cimma makwani biyun da suka gabata tsakanin sudan da kuma sudan ta kudu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu