1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar shugaban kristocin Coptic a Masar

March 18, 2012

Dubun dubatan 'yan darikar Coptic sun taru a Alkahira babban birnin Masar domin yin ban kwana da shugabansu wanda ya rasu da shekaru 88

Egypt's Coptic Christian leader Pope Shenouda III looks on during a gathering celebrating the 40th year of the his papacy, in Cairo, Egypt, Monday, Nov. 14, 2011. (Foto:Amr Nabil/AP/dapd)
Paparoman darikar Coptic Shenouda IIIHoto: AP

Da yammacin jiya asabar ne Paparoman darikar Coptic a Masar wato Pope Shenuda na uku ya rasu, shugaban addinin na Krista marasa rinjaye a Yankin Gabas Ta Tsakiya ya rasu ne yana da shekaru 88 da haihuwa. Cocin na Coptic ta sanar da cewa shugaban ya rasu ne bayan da yayi fama da rashin lafiya na tsawon shekaru da dama, kana kuma ba da dadewan nan ba, ya daina karbar magunguna cutar hantar da ke damun sa. Tuni dai shugabanin kasa da kasa suka fara aikawa da sakonnin ta'aziyya. Shugaba Barack Obama na Amurka, ya mika sakon ta'aziyyar sa zuwa ga iyalan Paparoman wanda ya kwatanta sa a matsayin mai fafutukar ganin an sami zaman lafiya tsakanin addinai ta hanyar tattaunawa. Kawo yanzu dai ba'a riga an fadi lokacin da za'a yi janaizar shugaban addinin wanda aka nada sa a matsayin Paparoma Alexandria a shekarar 1971 ba, kuma har wa yau Limaman Cocin ba su riga sun zabi wanda zai maye gurbin sa ba.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar