1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar sojojin Yemen a kudancin ƙasar

July 7, 2011

Masu tsananin kishin addinin musulunci na Yemen sun kashe sojojin ƙasar goma lokacin da suka yi wata kwantar ɓauna a kudancin ƙasar.

Dakarun ƙasar Yemen a cikin wata motaHoto: picture-alliance/ dpa

Sojojin Yemen goma sun rasa rayukansu a kudancin ƙasar a wani hari na kwantar ɓauna da ake kyautata zato mambobin ƙungiyar al-Qa'ida ne suka kai. Wata kafar da ke da nasaba da jami'an tsaron ƙasar ta nunar da cewar wasu masu tsananin kishin addinin musulunci sun buɗe wuta ranar laraba da maraice akan wata mota da ke ɗauke da sojojin goma da ke sanye da fararen kaya a garin Loder da ke zama matattarar 'yan al-Qaida.

Ƙungiyar al-Qaida na ci gaba da haɓaka a kudancin Yeman tun bayan da guguwar neman sauyi ta kaɗa a ƙasar a farkon wannan shekarar da muke ciki. A halin yanzu ma wata ƙungiya da ke kiran kanta "mai rajin kafa shari'ar musulunci" da kuma ke da alaƙa da al-Qaida ta na fafatawa da sojojin gwamnati a ƙoƙarin mayar da yankin ƙarkashin kulawarta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar