1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Myammar ta kakaba dokar tilasta wa matasan kasar aikin soja

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 10, 2024

Sojojin da suka yi juyin mulki a shekarar 2010 ne suka bijiro da dokar, wadda ka iya tsawaita wa'adin aikin sojan zuwa shekaru 5, kuma dokar ta yi tanadin hukuncin daurin shekaru 5 ga duk wanda ya ki shiga aikin sojan

Hoto: AP

Sojojin da ke mulki a Myammar sun kakaba dokar tilasta aikin soja na tsawon shekaru biyu, ga matasan kasar maza 'yan shekaru 18 zuwa da 35, sai kuma mata da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 27, domin taimakawa kasar wajen kawar da masu adawa da ita a cikin gida.

karin bayani:An mayar da Myanmar saniyar ware a jerin kasashen kungiyar ASEAN

Myammar dai ta fada cikin rudani tun bayan da sojojin suka yi juyin mulki a shekarar 2021, inda masu rajin kare Dimukradiyya ke ci gaba da jagorantar zanga-zangar adawa da sojojin.

Karin bayani:Aung San Suu Kyi ta kira Rohingya 'yan ta'adda

Sojojin da suka yi juyin mulki a shekarar 2010 ne suka bijiro da dokar, wadda ka iya tsawaita wa'adin aikin sojan zuwa shekaru 5, kuma dokar ta yi tanadin hukuncin daurin shekaru 5 ga duk wanda ya ki amsa kiran shiga aikin sojan.