Jana'izar matashiyar da ta mutu a zanga-zanga
March 4, 2021Komai zai dai-daita, kalmar da ta karade shafukan sada zumunta a duk fadin kasar Myanmar a wannan Alhamis kenan, a yayin jana’izar Kyal Sin mai shekaru 19 da sojoji suka bindige, a cikin masu zanga-zanga a yankin Mandalay, birnin na biyu mafi girma a kasar. Mako guda gabannin mutuwarta, matashiyar ta yi fice da rubutun da ta yi a bayan rigarta na cewa ''Muna son dimukuradiyya adalci ga Myanmar a martaba zabinmu“ A cewar Christine Schraner Burgener babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya a Myanmar, ba za su taba manta wannan rana da aka kashe mutane bila adadin ba.
Karin Bayani: An tarwatsa masu zanga-zanga a Myanmar
Mutuwar wannan matashiya cikin mutane kimanin talatin da takwas da aka harbe, na ci gaba da zama abin da 'yan Myanmar ke takaici a kokarin neman 'yancin mayar da kasar tafarkin demukuradiyya. Zargin 'yan sandan da amfani da makamai a kan masu zanga-zangar, na daga cikin abin da ke daga hankalin Majalisar Dinkin Duniya a cewar jami'a Christine.
Ko a wannan Alhamis, 'yan kasar da dama da ke adawa da juyin mulkin, sun ci gaba da jerin gwano suna rera wakokin jajen mutuwar 'yar uwarsu, inda ma suke cewa ba za mu manta ba har illa masha Allahu, a gefe guda wasu rike da allunan rubutun dauke da sunan gwarzuwa, suna raka gawar. To ina tasirin matakin da Kungiyar EU ta dauka kan sojojin da suka kifar da mulkin Aung San Suu Kyi na Myanmar da kuma yunkurin Majalisar Dinkin Duniya na kawo karshen rigimar? Christine ta ce, sojojin Myanmar, na cigaba da yin watsi na kiraye-kiraye a ciki da wajen kasar na sako Shugaba Aung San Suu Kyi da suka tsare bayan kifar da gwamnatinta saboda zarginta da magudin zabe.