Daurin sheraru bakwai ga 'yan jarida a Bama
September 3, 2018Talla
An yanke hukunci ga 'yan jaridun biyu bayan da aka zarge su da laifin wallafa asirin kasa kaman yadda alkalin wannan kotun Ye Lwin, ya sanar a lokacin da yake zartas da hukuncin. 'Yan jarida biyu da ke 'yan kasar ta Myanmar ko Bama, sun kasance a tsare tun daga watan Disamba na shekarar da ta gabata ta 2017 bayan da suka gudanar da wani bincike kan kisan kiyashin da sojojin kasar suka yi wa Musulmin kasar 'yan kabilar Rohingya.
Tuni dai ake kallon wannan hukunci a matsayin wani abu da zai kara dakushe martabar shugabar gwamnatin Kasar wanda a baya ta samu kyautar yabo ta Nobel na zaman lafiya Aung San Suu Kyi. Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da saki wadannan 'yan jarida ba tare da bata lokci ba.