Myanmar: MDD na son a gyara sansanoni
January 24, 2018Talla
Wata tawagar kasa da kasa da ta ziyarci wasu sansanonin da ke kusa da kan iyakar kasara Myanmar da Bangaledesh sun ce gidajen jama'a ba sa kan tsarin da dan adam zai yi rayuwa a ciki.
Gwamnatin Myanmar na ci gaba da jan kafa wajen tantance dubban 'yan kasar da ake shirin maido su gida daga kasashen da suke gudun hijira, amma MDD ta nun shakku kan ingancin tsaro kan rayuwar wadanda za a dawar.
Hukumomin kula da 'yan gudun hijira na MDD sun kiyasta sama da musulman Rohingya dubu 600 rikicin jihar Rakhine ya tilasta musu tserewa zuwa kasar Bangaledesh tun a watan Agustan shekarar 2017.