1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Na ci gaba da kirga kuriu a Zambia

September 29, 2006

Ana ci gaba da kirga kuriu a da aka kada a kasar Zambia,bayan jamaa da dama sun jefa kuriunsu a zabukan yan majalisa da kuma na shugaban kasar.

Rahotanni sun nuna cewa shugaba mai ci yanu Levy Mwanasa,wanda yayi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyoyin hakar maadinai da kuma yafe basuka,yana fuskantar kalubale mai karfi daga abokin adawarsa Michael Sata.

Michael Sata a nashi bangare ya nuna rashin jin dadinsa game da masu saka jari na waje da kuma talauci daya bazu tsakanin jamaar kasar.

Babu dai tabbacin ko yaushe zaa baiyana wanda ya lashe zaben.

Dokokin kasar ta Zambia kuma sun hana kafofin yada labarai na cikin gida yin tsinkayi akan sakamakon wucin gadi.

Ana sa ran zaa kammala kirga kuriun gobe asabar zuwa lahadi idan Allah ya kai mu.