1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhimancin nada rawani a cikin al'adun Abzinawan a Niger

Tila Amadou daga NijarFebruary 4, 2015

Azawa ko nada rawani na daya daga cikin manyan al'adu masu muhimanci a wasu kabilu na kasar Nijar, kamar kabilar Abzinawa da Toubawa da Larabawa

Niger Tende Festival in Zinder
Hoto: DW/L. Mallam Hami

Wannan sanannen abu ne musuman cikin kabilun da mafi yawan rayuwar su na cikin karkara , bayan shi kuma nada rawani na da muhimanci a wajen sarakuna da ma manyan Malamai.

Azawa ko nada rawani na da bambanci a tsakanin Kabilu inda ko wace kabila ke da irin nata ,misali a jihar Agadez a wajen Kabilar Abzinawa nadin ko azawa ya sha bambam alal misali nadin ko azawa na abzinawan yankin Air ya sha bambam da na yankin Azawak da dai sauran su.

Hoto: DW/L. Mallam Hami

A duk lokacin da saurayi ba'abzine ya kai shekara 18 , a kan yi baban buki na aza mishi rawani , inda a ke gayyata Manyan Malamai da datijawa , wadanda za su sheda cewa wanan yaron ya shiga sahun manya masu bada shawarwari a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Haka zalika diya Matan Abzinawa su ma a lokacin da su kai shekaru 18 a kan yi bukin daura musu Turkudi cewa da dan kwali na Abzinawa , tun daga ranar da a ka daura wa yarinya wanan turkudin ba za a sake ganin kwayar gashin ta ba.