1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sababbin hafsoshin tsaro

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 28, 2021

Bayan tsawon lokaci suna dako, a karshje dai burin da dama daga al'ummar Najeriya ya cika bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kori manyan hafsoshin tsaron kasar tare da nada sababbi.

Nigeria | Präsident Muhammadu Buharitrifft neue Militär Chefs in Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da sababbin manyan hafsoshin tsaron kasarHoto: Ubale Musa/DW

An dai kwashe tsawon lokaci ana bayyana bukatar shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya sallami manyan hafsoshin tsaron kasar, wadanda ake ganin sun gaza magance matsalolin tsaron da ya dabaibaye ta. A wannan karon dai shugaban ya amsa kiraye-kirayen, inda ya sanar da sauke hafsoshin tare da nada wasu sababbi. Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro ke kara dagulewa ba kawai a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar da Boko Haram tai kamari ba, har ma da sauran yankunan Arewacin kasar.

Wadanda aka nada dn dai sun hadar da Manjo Janar Leo Irabo wanda shi ne sabon babban hafsan tsaro da kuma ya taba rike rundunar wanzar da zaman lafiya da ake kira Operation lafiya Dole wacce ke zama babbar shalkwatar yaki da ta'addanci da kuma kwamandan rundunar hadin gwiwa ta kasashen gabar Tafkin Chadi. Sai kuma Manjo Janar Ibrahim Attahiru wanda ke zama sabon hafsan sojojin kasa na Najeriyar wanda shi ma ya rike rundunar ta Opertaion lafiya Dole. Sauran su ne Real Admiral A Z  Gambo shugaban rundunar sojan ruwa yayin da Air Vice Marshal A.O Amao ke zaman shugaban sojan sama.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna