1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nadin sabon Firaminsta a Masar

July 9, 2013

Bayan amai da gwamnatin rikon kwaryar Masar ta yi ta lashe kan nadin Firaminista, yanzu ta amince da Hazem Beblawy a matsayin Firaministan kasar.

Hoto: Reuters

An nada Hazem Beblawy wani masanin tattalin arziki, a matsayin sabon Firaministan kasar Masar a sabuwar gwamnatin rikon kwarya da aka kafa bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaba Muhammad Mursi.

Hazem Beblawy dai ya kasance Ministan harkokin kudi na kasar a lokacin mulkin soja daga watan Yuli zuwa Nuwamban 2011.

A hannu guda kuma an zabi jagoran adawar kasar wanda ya taba lashe kyutar zaman lafgiya ta Nobel Mohammed ElBaradei, a matsayin mataimakin shugaban kasa a gwamnatin ta rikon kwarya da za ta jagoranci gudanar da sabon zabe a kasar, nan da watanni shida masu zuwa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

ElBaradei dai shine tsohon shugaban hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta duniya, kuma an hakikance cewa shine ya hada kan 'yan adawar kasar da suka jagoranci kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Masar Hosny Mubarak.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita. Saleh Umar Saleh