1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NAFDAC ta amince da samar da rigakafin zazabin cizon sauro

Binta Aliyu Zurmi
April 18, 2023

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya wato NAFDAC a hukumance ta amince wa jami'ar Oxford da ke Birtaniya samar da rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na malariya R21.

DW Premium News | Thumbnail | Could climate change exacerbate malaria?
Hoto: DW

A cewar hukumar ta NAFDAC za a fara samar da rigakafin ne karkashin sharuddan yaki da cutar malariya da hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta samar.

Amincewar fara samar da rigakafin dai na zuwa ne ko kafin a kammala zagaye na uku a matakin gwajin rigakafin, to sai dai NAFDAC ta bukaci a fadada gwajin rigakafin har ya zuwa mataki na 4 da ma samar da cibiya samar da rigakafin a Najeriya.

Wannan mataki dai na da zummar kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro da ke hallaka sama da mutun 600,000 a kowace shekara a kasar da ke da mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Ko baya ga Najeriya kasar Ghana ta sanar da amincewar a fara samar da rigakafin zazabin cizon sauro a makon da ya gabata.