Shekaru 74 da kai harin nukiliya a garin Nagasaki
August 9, 2019Talla
A wannan Juma'a, Japan ke taron cika shekaru saba'in da hudu da Amurka ta kai wa birnin Nagasaki hari da makamin nukiliya. Magajin garin birnin Tomihisa Taue, ya baiyana takaici kan yadda kasashen Amirka da Rasha suka yi biris da kiran jama'ar da suka tsira daga harin suka yi, na daina kera makaman nukiliya. Ya gayyaci shugabanin kasashen duniya da su kawo ziyara kasar don gane wa idanunsu irin ta'asar da makamin ya haddasa.
Jama'a daga sassan kasar ne suka hallaci taron kafin a gudanar da addu'oi da kuma yin tsit na minti guda don girmama mamatan. Mutum fiye da dubu saba'in ne suka mutu a sanadiyar harin da Amirkan ta kai da makamin nukiliyan.