Najeriya: An bude makarantu a wasu jihohin kasar
October 5, 2020Tun bayan rufe makarantu tsawan lokaci a Nigeria sakamakon cutar Coronavirus, a yau Gwamnatin jihar katsina dake arewacin kasar ta bude makarantun jihar na Gwamnati da masu zaman Kansu domin cigaba da koyo da
Sakamakon wannan Cuta ta Covid-19 wadda ta janyo rufe makarantun yasa su kansu malamai sun gaji da zaman gida abin da yasa ana komawa makarantar suka fara aiki gadan-gadan acewar Lawal Lawal Kurfi shugaban makarantar jeka ka dawo bangaren jiniya dake kofar sauri a jihar Katsina
To ko wane tsari mahukuntan jihar suka yi game da yanayin zangon karatun Farfesa Badamasi Charanci shi ne kwamishinan Ilmin Jihar ta Katsina.
"Mun ba da sati uku a wannan zangon karatu. Sati biyu na farko a maimaita abin da aka yi a baya sati daya kuma a yi jarrabawa wanda shi ne zai kawo karshen zangon karatun na biyu. Sannan za a rufe zangon karatuin a ranar 23 ga watan Oktoba 2020".
Kwamishinan Ilmin ya kara da cewa za dawo makaranta a ranar 26 ga watan Oktoba domin cigaba da zangon karatu na uku har zuwa 5 ga watan Fabrairu 2021.
Dalibai dai a jihar Katsina na cigaba da nuna jin dadinsu kan bude makarantun
Domin tabbatar da cewa ana bada tazara a azuzuwa mahukunta a jihar sun raba makarantun jihar gida biyu wasu daliban su je da safe zuwa 12:30 wasu kuma su je daga rana zuwa yamma domin kare lafiyar su