1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Tura agaji zuwa yankin Nagorno-Karabakh

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 29, 2023

Yayin da 'yan asalin Armeniya da ke yankin Nagorno-Karabakh ke ci gaba da tserewa, Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da aniyarta ta tura tawaga a karshen mako domin ganin irin agajin jin-kan da ake bukata.

Armeniya | Nagorno-Karabakh | Gudun Hijira | UNCHR | Majalisar Dinkin Duniya
Mutane da dama na ci gaba da tsere wa daga yankin Nagorno-Karabakh zuwa ArmeniyaHoto: Vasily Krestyaninov/AP/dpa/picture alliance

Kakakin Majalisar Dinkin Duniyar Stephane Dujarric ne ya sanar da hakan, inda ya ce sun cimma yarjejeniya da gwamnatin Azerbaijan domin tura tawagar zuwa yankin da ya ce rabon da majalisar ta shige shi ya kai kimanin shekaru 30. A hannu guda kuma Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar UNCHR ta sanar da cewa kimanin mazauna yankin na Karabakh dubu 89 ne suka tsere zuwa Armeniya, adadin da ta kwatanta da kusan rabin yawan al'ummar yankin baki daya. Hukumar ta UNCHR ta ce tun bayan da kazamin fada ya rincabe a makon da ya gabata, adadin mutanen da ke tserewa daga yankin ya karu kuma akawai fargabar adadin nasu ya kai dubu 120 a 'yan kwanakin da ke tafe.