1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabuwar dokar agaza wa 'yan sanda a kan aikin su

Uwais Abubakar Idris AH
January 13, 2025

A Najeriya ana maida murtani a kan matakin da rundunar ‘yan sandan kasar ta dauka inda ta bayyana cewa kin taimaka wa jami'an 'yan sanda a lokacin da suke gudanar da aikin su ko kawo musu cikas laifi ne.

Nigeria | nigerianische Marine | Unabhängigkeitsparade zum 62. Jahrestag in Abuja
Hoto: Emmanuel Osodi/AP Photo/picture alliance

 Karuwar yawaitar zargi na cin zarafin ‘yan sanda a bakin aikin su da kokari na hana su gudanar da aikin su musamman in batu kama wadanda ake zargi da aikata laifi ya taso da wannan batu.

Musamman damar amfani da kafofin sada zumunta da ya ba da damar yada irin wadannan abubuwa.

Wannan ya sanya rundunar ‘yan sandan Najeriyar bayyana cewa ta yi hir da irin wannan halayya da ba za su lamunta ba, domin dokar aikin ‘yan sanda a Najeriya ta yi tanadi na hukunci a kan lamarin.

Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Amma me dokar ‘yan sanda musamman sashi na 98 ta tanada da ake maganar, dokar ta tanadi tara ta Naira dubu  500 ko daurin watanni shida ga duk dan Najeriyar da yaki taimaka wa ‘yan sanda gudanar da aikin su ko kawo musu cikas. Barrister Buhari Yusuf lauya ne mai zaman kansa da ke Abuja.

 Dangantaka dai ta dade da yin tsami tsakanin ‘yan sanda da sauran jama'a a Najeriyar duk da kokari na kafa kwamitin na musamman a kan kyatata dangantaka tsakanin fararen hula da ‘yan sanda a daukacin jihohi da ma wasu yankunan kasar. 

Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

An sha fuskantar hali na yi bai wa ‘yan sanda taron dagi da jama'a kan yi masu attire, wani lokacin a lakada musu duka. To sai dai ga Imran Wada Nas shugaban rundunar adalaci da ke fafautukar kwatarwa yan kasar 'yanci yace ‘yan sanda su duba kan su tukuna.

Zarge-zarge irin  wadannan dai lamari ne da ke sanya ‘yan sanda kokari na kare kan su bisa abin da doka ta tanadar musu. 

To sai dai lamari ne na dokar aiki da ta tanada da taimaka wa ‘yan sandan su gudanar da aiki, abin da kakakin rundunar yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa babu batu na yake hakin kowa sai dai bin doka da oda kawai.

Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Shin wane tasiri wannan mataki na kara jadada aiki da sashi na 98 na dokar ‘yan sanda zai yi wajen kyautata aiki da ma dangataka tsakanin ‘yan sanda da sauran  jama'a?