Najeriya: Adawa da mayar da shugaban NHIS
February 12, 2018Korafin hukumar kula da inshorar lafiya NHIS na zuwa ne a daidai lokacin da ake takaddama a kan matakin shugaban kasar Muhammadu Buhari na sake mayar da shugaban hukumar Farfesa Usman Yusuf a bakin aikinsa, watanni bakwai da dakatar da shi bisa zargin cin hanci da rashawa.
Tun bayan bankado batun rashawar ake ta cece-ku-ce kan makomar hukumar da ake zargi da nuna gazawa a harkokinta na kulawa da miliyoyin mara lafiya. A taron ‘yan jaridu da ya gudana a ranar Litinin a Abuja fadar gwamnatin kasar, shugabanin hukumar sun yi kokari na bayyana zahirin halin da ake ciki a kan batun inshorara lafiya ta Najeriya da yanzu shekaru 13 da kafa wa.
Yanzu dai ta kai ga an girke jami’an tsaro a kofar shiga hukumar domin kaucewa dauki ba dadi na kungoyin ma’aikata da ke nuna adawa da maida shugaban hukumar a bakin akinsa. Tun kafin wannan lokaci majalisar wakilan Najeriya ta bayyana cewa dole ne a mayar da shugaban a bakin aikinsa.
Najeriya na matukar bukatar zaburar da aikin hukumar samar da inshorar lafiya ta kasar, abin da kwararu ke bayyana zai iya tasirin wajen kyautata samar da lafiyar jama’a.