1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na fama da karancin jami'an tsaro

December 28, 2021

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce, rashin isassun jami'an tsaro a Najeriya, na daga cikin abin da ke kawo cikas wajen magance matsalar tsaron kasar.

Nigeria Polizeikräfte in Lagos
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Gwamna Aminu Bello Masari ya ce, ya zama wajibi al'umma su tashi su nemi makamai don kare kansu. Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a jahar Katsina da ke arewacin kasar, a daidai lokacin da ake shirin bankwana da shekarar 2021 me karewa. 

Karin Bayani: Najeriya: Karfin sojoji ya kusa kare wa

Gwamnan ya kuma kara da cewa, idan akai kididdigar jami'an tsaro da ke akwai a Najeriya, sun yi matukar yin kadan, duk da cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara daukar karin jami'an tsaro, domin taimakawa wajen magance matsalar. Rahotanni sun nuna yankunan da dama musamman a jihar Katsina sun samu saukin hare-haren sakamakon yadda jama'a ke hana idanunsu bacci idan dare ya yi don kare garuruwansu. 

Matsalar garkuwa da mutane tayi kamari a Najeriya Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Matsalar tsaron Najeriya musamman na yankin Arewacin kasar na ci gaba da daukar hankulan duniya, inda a can kasar Amirka, 'yan asalin Najeriya mazauna Amirka suka sake yin kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta sauke nauyin da ke kanta, na tabbatar da tsaron rayukan al’umma.

Karin Bayani:  Najeriya: Shawo kan matsalar tsaro

Cikin wata sanarwa da kungiyar mai suna DANGI USA ta fitar a birnin Washington, ta yi Allah wadai da sakacin da gwamnatin Najeriya take yi, a yayin da ake ci gaba da kashe rayukan talakawa, da barnata da dukiya da satar mutane ba kaukautawa, musanman a yankin arewacin kasar.

Karin Bayani: Najeriya: Martani kan kare kai daga 'yan bindiga

Tsaron arewacin Najeriya na kara muni Hoto: Nasiru Salisu Zango

Kungiyar DANGI ta ce, kodayake akwai jami’an tsaro masu kishi da suke son yin aikin ceto Najeriya, amma ya zama wajibi, su ma sauran ‘yan kasa, su rika taimaka masu, sannan a rika hukunta dukkan ‘yan ta’addar da aka kama ba wai a saki wasun su ba.

Daga karshe kungiyar ta ‘yan arewa mazauna Amirka, ta sake yin jaje da nuna alhini ga dukkan mazauna Najeriya musanman a arewacin kasar da suke shan ukuba da kuma wadanda suka rasa 'yan uwa da danginsu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani