Bala'iNajeriya
Ko za a kawo karshen ambaliya a Najeriya?
May 30, 2025
Talla
Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Niger SEMA Ibrahim Audu Husseini ne ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, adadin ya kai sama da 100 bayan da aka sake gano gawarwakin mutane. Hukumar ta SEMA ta sanar da cewa mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe tsawon daren Larabar wannan mako ana yi, ya yi awon gaba da gidaje sama da 50 a birnin na Mokwa da ke tsakiyar jihar ta Niger. Da ma dai Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NIMET ta yi gargadin samun mamakon ruwan sama a jihohi 15 na kasar, cikinsu har da jihar ta Niger.