1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Lalacewar amfanin gona a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 22, 2022

Yayin da manoman Najeriya ke daf da girbe amfanin gona, ibtila'in ambaliyar ruwa da ya sako wasu jihohin kasar gaba ya salawantar da dimbin amfanin gona.

Najeriya | Katsina | Ambaliyar Ruwa
Jihohi da dama musamman a arewacin Najeriya, na fama da bala'in ambaliya ruwaHoto: DW/Y. Ibrahim

Jihar Jigawa da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriyar, na daga cikin jihohi na baya-bayan nan da ambaliyar ruwan ta shafa a Tarayyar Najeriya. Ambaliyar dai na ci gaba da yin mumunar barna a sassan Najeriyar da dama, inda a jihar Niger ambaliyar ta yi awon gaba da kabarurruka sama da 500 a garin Mariga tare da lalata gidaje da gonaki da dama a garin Kontagora da Rafi da ma wasu sassan jihar.

Tuni mai dai Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriyar NEMA ta ce Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa ta kasar Hydrological Services ta yi gargadin cewar, sakamakon saukar mamakon ruwan sama a kai-a kai da cikar Kogunan Niger da Benue da kuma ruwan da ya balle daga dam din Lagdo na Kamaru wajibi ne a gaggauta kwashe wasu al'ummomi daga matsugunansu.

Jihohin da al'ummominsu ke kan gaba wajen fuskantar wannan barazana ta ambaliyar ta ruwa dai, sun hadar da Rivers da Delta da Cross Rivers da Bayelsa da Edo da Anambra. Haka kuma bayanan hukumar ta NEMA sun nunar da cewa ambaliyar ruwan, za ta fi yin muni a jihohin Taraba da Nasarawa da Benue da Adamawa da Niger da kuma Kebbi.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna