1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Amfani da kafofin sada zumunta don bunkasa noma

October 11, 2017

Sabon shirin horas da manoma hanyoyin shiga shafukan sada zumunta don tallata kayan amfanin gonarsu.

Messenger-Dienste
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Kastl

A sakamakon ci-gaban kimiyya da fasaha ta ko ina a Tarayyar Najeriya, yanzu haka wata kungiyar kwararrun masana kimiyya a kasar ta bullo da wani sabon shiri irinsa na farko wajen horar da manoma sabbin dabarun hanyoyin shiga kafafen sadarwa na zamani da zumar tallata kayayyakin gonakinsu da sauran hajar su a kyauta.

An yi hakan ne don tabbatar da ganin manoman Najeriya na tafiya da hikimomi da fasahohin zamani kamar sauran takwarorinsu na kasashen duniya. Za su rika daukar hotunan kayayyakin amfanin gonarsu domin sayarwa a shafukan dillalan kayan gwari da sauran kayan abinci a yanar gizo.

Tuni dai manoma a wasu kasashen Afirka kamar wannan manomin a kasar Kenya, suka fara tallata hajarsu ta kafafan intanetHoto: Jeroen van Loon

Mr Adikpe Odeh shi ne dai shugaban kungiyar mai suna IHIFIX Technology Nigeria da ya ce "shirin na da matukar fa'ida ga manoman wannan Najeriya domin zai taimaka masu ta hanyoyi dabam-dabam na magance irin hatsarin da manoman ke fadawa ciki, musamman ma irin asarar da dillalai ke janyo masu da kuma rage yadda suke shan wahalar fitowa da kayayyakin daga gonakinsu."

Mr Adikpe ya ce amfani da fasahohin zamani wajen bunkasa harkar noma a duniya na farfado da darajar amfanin gona, domin ko da manomi ya sanya kayan ba a saya ba, kayan gonansa na tare da shi. Saboda haka ne ma ya janyo hankalin manoma wajen shiga kafafen sadarwa domin neman kungiyoyin dillalan kayayyakinsu.

A zantarwar da tashar DW ta yi da wasu manoma sun nunar da cewa wannan ci-gaba ne aka samu babba. To sai dai matsalar ita ce yadda za su rika cajin wayoyin hannunsu, sannan kuma suna da fargaba 'yan damfara ka iya kawo tsaiko.

Sai dai masanan sun ce burinsu shi ne na ganin manoma sun rage tafka asarar da kuma magance yadda dillalai ke cin kazamin riba fiye da manoman.