1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar zaben 'yan takara na jam'iyyu a Najeriya

May 26, 2022

Masana a fannin siyasa sun bayyana munmunar hatsarin da ke tattare da yadda ake amfani da kudi wajen sayen wakilan jami'yyu da ke zaben 'yan takara.

Gabanin zaben 2023, kasuwar delegates ta bude a Najeriya.
Gabanin zaben 2023, kasuwar delegates ta bude a Najeriya.Hoto: Getty Images/AFP/L. Tato

A Najeriya a dai dai lokacin da jam'iyyun siyasa ke ci-gaba da gudanar da zaben fidda da gwani da tantance 'yan takara, kungiyoyin fararen hula da masu gwagwarmayar dorewar mulkin dimukradiyya na nuna damuwarsu bisa ga yadda ake anfani da miliyoyin kudade wajen sayen wakilan zaben fidda gwani wato delegates,

Yanzu haka dai batun amfani da makuddan kudi wajen zaben fidda gwani da dukan jami'yyun da ke a fadin ke gudanarwa, shi ne dai babban batun da ya karade kafafen watsa labarai, kuma da ke ci-gaba da janyo zazzafar muhawara tsakanin ‘yan Najeriya dangane da irin wannnan sabon salon yanayin siyasar kasuwanci ta hanyar sayen wakilan. 

Masu zabe a birnin AbujaHoto: DW/Uwaisu A. Idris

Rahotanni sun yi nuni da yadda 'yan takara na sayen masu tantance su daga Naira miliyan biyar zuwa sama. An kuma ga yadda su kansu delegates din suka koma sanyawa kansu farashin miliyoyin kudade ga dukkanin 'yan takaran da ke neman wata kujerar siyasa.
'Yan Najeriya dai na ganin cewa lallai dai kam akwai bukatar kara bullo da sabbin hanyoyin wayar da kai musanman ma dai ga wadanda aka dorawa alhakin zaben fidda gwani a kan hanyoyin sauke hakkin da ya wajaba a kan su.

Kada kuri'a a cibiyar zabeHoto: DW/Uwaisu A. Idris

Da yawa daga cikin wadanda tashar DW ta zanta da su sun nuna takaicinsu bisa ga yadda delegates suka maida hankalin kacokam a kan harkar neman kudi maimakon dai sauke nauyin da aka basu na tantance ‘yan takara da suka cancanci wakiltar jam'iyyar a dukkanin zabubbukan da ke tafe. 

A jihar Kaduna dai wasu 'yan takaran da suka sha kaye,sun koma bin wadanda suka karbi kudadensu, lamarin da ke nuni da cewa wasu da dama kudaden bashi ne suka ciyo daga wasu wurare, abun kuma  da ke nuni da yadda ya janyo karancin kudaden kasashen ketare a Najeriyar musamman Dalar Amurka.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani