1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyara kan dokar zabe a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
November 10, 2021

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da sauye-sauyea dokar zabe, bayan daidaita wurarren da suka samu sabani da majalisar dattawa da kuma gwamnatin tarayya.

Nigeria National Assembly
Majalisa ta tara ta amince da gyaran dokar zabe a NajeriyaHoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Kanwa dai ta kar tsami a game da dokar zaben Najeriyar da aka dade ana fafatawa kan yi mata gyaran fuska, bayan samun daidaito tsakanin 'yan majalisar dattawa da takwarorinsu na majalisar tarayya kan dukkanin bambance-bambancen da ke tsakaninsu a kan dokar zaben.

Karin Bayani: Bukatar kammala gyaran dokar zabe a Najeriya

Muhimman batutuwan da aka samu sabanin a kansu tun da fari dai, sun hadar da aike wa da sakamakon zabe ta amfani da kafar Internet da hukunci mai tsanani ga masu magudin zabe da kuma mayar da shi ya zama doka da za ta tilasta dukkanin jamiyyun siyasa su yi amfani da tsarin zaben 'yar tinke wajen zaben fidda gwani ko 'yan takara. Ana dai yi wa jamiyyar APC mai mulki kalon wacce tun farko ta yi uwa da makarbiya a amfani da wannan tsari na 'yar tinke.

Jam'iyyar PDP, na zaman babbar jam'iyyar adawa a NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

A yayin da 'yan majalisar ke jinjinawa kansu tun kafin aje ko ina, jam'iyyar adawa ta PDP da ma APC mai mulki na ganin akwai sauran rina a kaba. Tuni dai PDP ta fitar da sanarwa kan dokar zaben fidda gwani da ta ce ba ta gamsu ba. Bayanai sun tabbatar da cewa ita kanta jam'iyyar APC ta kira wani taron sirri da 'ya'yanta da ke majalisardattawan, inda jami'an jam'iyyar suka nuna damuwa kan gyare-gyaren da majalisar ta yi wa dokar zaben.

Karin Bayani: Shirin sauya fasalin tsarin zaben Najeriya

A yanzu dai, majalisar za ta tura da wadannan gyare-gyare zuwa ga shugaban Najeriyar domin ya rattaba masu hannu. Idan har aka rattaba hannu kan dokar, majalisar ta tara za ta kasance wacce ta kafa tarihi a kan kokari na yi wa tsarin zaben Najeriyar gyara domin samun ci gaba mai ma'ana.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani