Daliban Kagara sun dawo gida
February 27, 2021Talla
Mutanen da suka hada da daliban makarantar gwamnati da malamansu, sun fada hannun wasu maharan ne da suka yi awon gaba da su. Gwamnan jihar Niger Najeriya ya bayyana a shafinsa na Twitter da cewar an sallamo daliban kana kuma ma har mahukunta sun gana da su. Sai dai sakin daliban na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan bindiga ke ci gaba da garkuwa da wasu daliban makaranta fiye da 300 da suka sace a wata makarantar gwamnati ta Jangebe da ke karamar hukumar Talatar Mafara ta jihar Zamfara, da ke fama da hare-haren 'yan bindiga.