1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An dage haramci kan Twitter

Ahmed Salisu
October 1, 2021

Gwamnatin Najeriya ta sanar da dage haramcin da ta sanya shafin sada zumunta na Twitter a kasar wanda aka yi a watannin baya.

Twitter Logo
Hoto: Imago Images/Zuma/O. Marques

Gwamnati Najeriya ta bayyana cewar ta janya haramcin da ta sanya kan shafin sada zumunta na Twitter da ta yi a watannin baya. Shugaban kasar Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka a jawabinsa ga al'ummar kasar albarkacin bikin cikar kasar shekaru 61 da samun 'yancin kai.

Shugaba Buhari ya ce haramcin zai tabbata ne kawai in har kamfanin na Twitter ya bi ka'idojin da gwamnatin Najeriya ta gindaya masa sau da kafa, ciki kuwa har da yin rijista tare kuma da biyan haraji a kasar.