Najeriya: An fara zaman majalisa da hatsaniya
September 29, 2015An dai fara zaman majalisar ne da jawabi daga bakin shugabanta Bukola Saraki wanda ya fara da tabo shari'ar da ake yi masa a kotun da'ar ma'aikata har ma ya danganta tuhumarsa da siyasa saboda a cewarsa wasu da ba sa so ya cigaba da kasancewa a matsayin shugaban majalisar ne ke da hannu a lamarin inda ya ke cewar dokokin Najeriya sun ba 'yan majlisa ikon zaben shugabansu maimakon wani daga wajen ya sanya musu baki a cikin sha'anin zaben.
Bayan kammala jawabin na Sanata Saraki, wasu daga cikin 'yan majalisar sun jefa kuri'ar jaddada goyon bayansu ga shugabancin nasa da na mataimakinsa Ike Ekweremadu da sauran masu rike da mukamai a majalisar. To sai dai wannan batu bai yi wa wasu 'yan majalisar dadi lamarin da ya jawo tada jijiyar wuya.
Hatsanitya dai ta kaure ne a lokacin da Sanata Kabiru Marafa ya jawo hakalin shugaban majalisar a kan rashin amincewarsa da matakin kada kuri'ar jaddada goyon bayan shugabancin Sarakin, batun da ya kaisu ga fadi in fadi tsakaninsu har ma shugaban ya bada izinin ficewa da Sanata Marafa din daga cikin zauren majalisar. A hirarsa da DW, Sanata Kabiru Marafa ya ce bai ga dacewar kada wannan kuri'a ta amincewa da shugabancin na Saraki ba har sau biyu cikin watanni uku.
Wannan hali da aka shiga dai ya sanya wasu daga cikin 'yan majalisar ciki kuwa har da Sanata Abu Ibrahim cewar ya kamata su gyatta tsarinsu don gudun fuskantar fushin al'ummar Najeriya. Yanzu haka dai 'yan Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakunansu kan wannan batu kana sun zuba ido don ganin kamun ludayin 'yan majalisar wajen tantance jerin sunayen mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ke son aiki da su a matsayin ministoci.