Najeriya: Sahihin daftarin dokar haraji ya bayyana
January 5, 2026
Matsin lambar da ya biyo bayan bankado zargin sauya wasu sassan na dokar harajin Najeriya ne ya sanya majalisar dokokin kasar fitar da sahihin daftarin dokokin guda hudu da majalisar ta yi, tare da watsi da wancan daftarin da aka wallafa a baya. Dokar haraji da aka fara aiki da ita a ranar daya ga watan Janairun nan ne tafi daukar hankali saboda gano cewa lallai an canza wasu sassan daga zahirin abinda majalisar ta amince da shi.
A yanzu majalisar dokokin Najeriya ta bayyana watsi da wancan daftari tare da cewa abinda ta fitar a yanzu shi ne sahihin daftarin dokar da za'a yi aiki da shi a Najeriyar. Dama can aikin majalisa ne ta wallafa dokar bayan shugaban kasar ya sanya mata hannu ba wai bangaren zartaswa ba.
Mataki ne na kwantara da hankali al'ummar Najeriya da suke zargin an yi kokarin yi masu sakiyar da ba ruwa a dokar harajin, kasar da ta bullo da sabon tsari na biyan harajida gwamnatin ta bayyana tsara shi don sanya attajirai biyan haraji tare da samar da sauki ga marasa karfi.
Daga majalisar zuwa bangaren zartaswa na fatan a yanzu kura ta kwanta a kan wannan al'amari inda tuni gwamnati ta fara aiki da sabuwar dokar harajin da ta tsara sai wanda ya kai matsayin samun albashi ko kudin shiga da suka zarta Naira dubu 800ne za su fara biyan haraji, ga kamfanonin kuma sai sun kai Naira milyan 50, abin da ya cire mafi yawan ‘yan Najeriyar daga biyan haraji a kasar.