1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake ya hallaka jama'a a Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
December 19, 2020

Wani harin kunar bakin wake da aka kai Konduga na jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya, ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku da raunata mutane biyu.

Nigeria Boko Haram
Hoto: Lekan Oyekanmi/AP Photo/picture alliance

Kamfanin AFP ya ruwaito wani kakakin 'yan kato da gora Ibrahim Liman na cewa, wata yarinya ce 'yar kimanin shekaru 17 ta tarwatsa bam da ke jikinta, a daidai lokacin da wani rukunin jama'a ke tsaka da taro a dab da harabar sarkin garin.

Duk da yake kawo yanzu ba wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, masana na cewa harin baya rasa nasaba da irin wadanda Kungiyar Boko Haram ta sha kai wa a yankin, wanda ko a shekarar 2019 wani harin makamancisa na Boko Haram da yan kunar bakin wake uku suka kai, ya hallaka wasu mutane akalla 30 baya ga raunata wasu da dama.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW