Sauki ga dillalan man fetur a Najeriya
May 7, 2020Wata sanarwar kamfanin cinikin mai na kasar dai ta ce an rage farashin da dillalan man fetur din za su biya zuwa naira 108 kan kowacce lita, wanda hakan ke nuni da cewa sun samu ragin kaso 17 cikin 100 a wwannan wata na Mayu da muke ciki. Sabon farashin dai na zaman ragi karo na uku cikin tsawon watanni biyun da suka gabata da kuma ake ta'allaka shi da yadda farashin gangar danyan man fetur din ya fadi a kasuwannin duniya. Tun a cikin watan Maris din da ya gabata ne dai Najeriyar ta fara ganin alamun sauyin, bayan da gwamnatin kasar ta rage farashin daga Naira 145 kan kowacce lita ya zuwa Naira 125.
Ko da a watan Afrilun da ya gabata, 'yan kasar sun biya naira 123 da kwabo 50 a matsayin farashin man fetur din kan kowacce lita, a wani abun da ke zaman ba sabun ba. A yanzu dai ana sa ran za a rinka sayan man a gidajen mai a kan Naira 117 kowacce lita.
Shi kansa farashin man diseal na manyan motoci na dakon kaya dai ya yi kasa, inda ake sayar da shi tsakanin Naira 164 zuwa 166 maimakon kusan Naira 200 da yake a gidajen man kasar. Kuma ko bayan al'umma ta kasa da suka share tsawon lokaci suna shan man fetur mai arha, su kansu dillalan man dai sabon ragin ya burge su. To sai dai kuma a yayin da ake tsallen murnar ragin farashin akwai dai tsoron komawa gidan jiya ga Tarayyar Najeriyar, da ke duban yiwuwar sake dagawa na farashi na bakar hajar a nan gaba.