1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An yi zanga-zanga kan dokar zabe

Ahmed Salisu
February 9, 2026

Daruruwan mutane a Najeriya sun yi zanga-zanga a majalisar dokokin Najeriya don nuna rashin jin dadinsu da matakin 'yan majalisar kan ki amincewa da aikewa da sakamakon zabe ta na'ura da zarar an kammala kidaya.

Nigeria Protest NLC Abuja
Hoto: Uwais/DW

'Yan kungiyoyin kwadago da na fararen hula da 'yan siyasa na adawa da masu rajin tabbatar da demokradiyya ne suka gudanar da zanga-zangar domin yin matsin lamba ga 'yan majalisar kan sake tunani game da batu.

Tuni dai 'yan kwadagon suka bayyana aniyarsu ta kauracewa zaben muddin ba su sake duba wannan lamari ba domin a cewarsu kin aikewa da sakamakon ta na'ura zai iya haifar da magudin zabe.