Rashin tsaro a arewacin Najeriya
June 18, 2020Za dai a iya cewa tura ta kai bango, domin kuwa tuni matasan yankin arewacin Najeriyar suka fusata har ma suka dauki matakin yin zanga-zangar lumana. An dai kaddamar da zanga-zangar a jiahar Katsina, guda daga cikin jihohin da hare-haren 'yan bindigar ya fi muni, jihar kuma da ke zaman mahaifar shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Matasan dai sun sha alwashin yin zanga-zangar a dukkanin jihohin kasar domin nuna takaicinsu da kuma yin kira ga mahukuntan kasar da su dauki matakan da suka dace, domin tsiratar da rayuka da dukiyoyin al'ummar da ke fuskantar sata da kisa da cin zarafi da fyade a hannun 'yan bindigar.
Sai dai abin takaici, rahotanni da ke fitowa daga Tarayyar Najeriyar, sun nunar da cewa an kame jagoran wannan zanga-zanga mai suna Nastura Ashir Sharif: 'Yan gudun hijira cikin tasku