Kotu ta yi watsi da karar Atiku kan zabe
October 30, 2019
A Najeriya, kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta PDP ta daukaka a gabanta, tana mai kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 watan Febuwarin da ya gabata, wanda dan takarar jam'iyyar APC Muhammadu Buhari ya lashe da kaso 56 daga cikin dari a yayin da abokin hamayyar tasa Atiku Abubakar ya samu kaso 41 daga cikin dari.
Babban alkalin kotun Tanko Muhammad ne ya bayyana wannan hukunci a wannan Laraba inda ya ce, sun yi watsi da karar ne domin kuwa zarge-zargen da hujjojin da jam'iyyar adawar ta gabatar ba su gamsar da kotun ba. Amma ya ce sai a nan gaba ne kotun za ta bayyana dalillan da suka sa illahirin alkalai bakwai na kotun suka yi watsi da karar jam'iyyar adawar.
Dama dai a tsakiyar watan Satumban da ya gabata, a matakin farko na shari'a, kotu ta yi watsi da karar da dan takararar adawar Atiku Abubakar ya shigar a gabanta domin neman a soke sakamakon zaben. Da wannan hukunci dai, kotun ta kawo karshen rikicin sakamakon zaben wanda aka share watanni takwas ana yi tsakanin manyan jam'iyyu biyu na Najeriyar a gaban kuliya.