Najeriya: Badakalar cin hanci a kamfanonin Shell da Eni
March 3, 2017Hukumar da ke yaki cin hanci da rashawa a Najeriya a ranar Alhamis ta gabatar da tuhumomi kan manyan kamfanoni da ke hakar albarkatun man fetir na Shell da Eni saboda badakalar cin hanci da rashawa kan wata rijiyar mai a teku badakala a harkar da ta kai Dala miliyan dubu daya da dubu dari uku. Hukumar EFCC na zargin hannun mutane 11 a cikin wannan badakala kamar yadda takardun kotu suka nunar.
Ana dai zargi kamfanonin na Shell da Eni da Agip wani reshe na Eni da bayar da cin hanci na kudin da aka yi kiyasin sun kai Dala miliyan 801 zuwa ga wasu 'yan kasuwa da 'yan siyasa kan kulla wancan harka.
Wannan dai shi ne bincike na baya-bayan nan tun bayan irin wannan badakala a harkar kasuwancin manfetir da aka faro tun a shekarar 2011lamarin da ya bayyana karara irin munana da ake aikatawa da wasu jami'ai a dukiyar kasa a Najeriya.