1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa yaki da cin hanci a Najeriya

Salissou Boukari
December 19, 2016

A wani abun da ke zaman yunkurin sake tabbatar da matsayinsa kan yaki da cin hancin a Tarrayar Najeriya, Shugaban Muhammad Buhari ya bada umarnin bincikar duk wani jami'in da ake zargi.

Nigeria Symbolbild Muhammadu Buhari Anti-Korruptions-Offensive
Hoto: picture-alliance/AP Photo/C. Owen

Kama daga sakataren gwamnatin kasar ya zuwa babban jami'in mulki a fadar shugaban kasar, sannan da shugaban hukumar yakar hanci ta kasar EFCC dai, an ambato da dama a cikin zargin cin hanci a bisa jami'an na gwamnatin ta Abuja. To sai dai kuma wata sanarwar fadar gwamnatin kasar na neman mayar da martani ga jerin zargin da ake yi tare da umartar ministan shari'a na kasar ya  kaddamar da bincike kan duk wani jami'in gwamnatin da ake zargi da karbar cin hanci a karkashin jagorancin na Buhari.

Hoto: Abddulkareen Baba Aminu

Duk da cewar dai sanarwar da kakakin fadar ta shugaban kasa mallam Garba Shehu ya kai ga fitarwa ba ta ambato adadi na jami'an da za su fuskanci binciken dama lokacin da ake shirin dauka kafin a kammala shi ba, ana dai kallon umarnin a matsayin aiken sako a bangaren shugaban kasar da sannu a hankali yake kallon yakin na fuskantar suka ta adawar da ke fadin ya rikide ya zuwa kokari na cin zarafin 'ya'yan bora a cewar Mallam Garba Shehu kakaki Gwanatin ta Abuja.

To sai dai kuma ko ya zuwa ina shugaban kasar yake iya burge masu adawa a kasar?  Daga dukkan alamu dai tuni sabon umarnin ya kama hanyar burge 'yan kungiyoyi fararan hula da ke fadin son barka a fadar Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman babban sakataren kungiyar fararen hula ta yammacin Afirka.

Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Akalla Naira Miliyan Dubu 565 ne gwamnatin kasar ta ce ta karba daga hannun wasu da ake zargin sun sace daga lalitar gwamnati a shekarar da ke shirin karewar, kuma ta na shirin kashe su cikin kasar a shekarar da ke tafe. Abun jira a gani dai na zaman tasirin da wannan bincike zai yi kan jami'an gwamnatin wadanda a baya ake yi wa kallon basu tabuwa.