Cikar shekaru 59 da samun 'yancin kan Najeriya
October 1, 2019Albarkacin ranar ta daya ga watan Oktoba na shekara ta 2019 da ke zama ta cikar shekaru 59 da Najeriyar ta samun 'yancin kanta daga Turawan Ingila, an share tsawon ranar ta wannan Talata ana biki ana cashewa a cikin fadar gwamnatin Tarrayar Najeriya da ke zaman masaukin baki na bikin 'yancin kasar na shekara 59 a duniya. An kuma gudanar da faretin ban girma tare da saki tantabaru na zaman lafiya duka a cikin bikin da ya gudana a birnin Abuja.
Bikin wanda ya samu halartar daukacin shugabannin madafan ikon kasar guda uku da ministoci da manyan jakadu na kasashen waje game da wasu a cikin tsoffafin 'yan mulkin na kasar dai na zaman mafi tasiri ga kasar da ke fuskantar muhimman kalubalen rashin tsaro da ma matsala ta tattalin arzikin al'ummarta. Abun kuma da ya dauki hankalin shugaban kasar Muhammad Buhari da tun da safiyar yau din nan ya yi wani dogon jawabi ga 'yan kasar. Jawabin na mintuna 25 ya kusan tabo matsaloli na kasar kama daga batun tsaron da al'adar yada jita-jita ta kafafen sada zumunta game kuma da matsalar tattalin arziki da ma matakan da kasar ke dauka domin tunkarar jerin matsalolin inda yake cewa:
"Kwanan nan na nada majalisar mashawarta ta tattalin arziki domin ba ni shawarar kan manufofi na tattalin arzikin da za su taimaki al'ummarmu. Wannan majalisa mai zaman kanta za ta yi aiki da shugabanni na ma'aikatu da hukumomi na gwamnati domin ganin ba mu karkace ba a kokari dora kasarmu zuwa ga arziki. Kuma zan ba da tabbacin cewar duk wata shawarar da ke da tsaurin gaske, to zan tabbatar da tasirinta bai tsanani ba tsakanin talakawa na kasa da su ne mafi fuskantar barazana ba su ji a jika ba”
Ga batun watsa jita-jita ta kafafe na zumunta kuwa shugaban ya ce gwamnatin kasar ta shirya tsaf domin sa kafar wando wuri guda domin kai karshen matsalar:
"Hankalinmu na komawa ga yaki da laifukan yanar gizo da kuma baza jita-jita ta kafafen sada zumunta. A yayin da muke mutunta 'yancin al'ummarmu na fadar albarkacin baki ko kuma zumunta, a inda wannan 'yanci ke zama barazana ga 'yanci na wasu ko kuma ke neman jefa kasar cikin barazanar rashin tsaro, to kuwa za mu dauki mataki mai karfi da kuma tasiri”
Buharin dai ya ce gwamnatin kasar tana shirin kammala muhimman ayyukan sauyin matsayi na kasar kamar yanhar Abuja zuwa Kano da madatsar ruwa ta Mambila game da titunan Legas zuwa Ibadan da kuma gadar Kogin Kwara ta Biyu kafin karshen shekara ta 2022.Sai dai shugaban ya ce ana bukatar sauyin halayya ta 'yan kasa da hadin kan kowa kafin kasar ta iya cimma wannan buri nata.
An dai kare bikin tare harba igwar ban girma 21, sannan kuma da shugaban kasar dubin faretin ban girman kafin daga karshe a yanka alkakin murnar ranar mai tasiri. Shekaru 59 dai na nufin abubuwa dabam-dabam ga mahalarta bikin. Boss Mustapha dai na zaman sakataren gwamnatin kasar da kuma ya ce shi kansa zaman kasar wuri guda na zaman babban ci-gaba. Sai dai kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Arc Namadi Sambo zaman lafiya na zaman babban burin da ya kamaci 'yan kasar su nema koyaushe. Ga Senata Ahmed lawal da ke zaman shugaban majalisar dattawa na kasar sun shirya tsaf da nufin tallafa wa gwamnatin kasar wajen samar da tsaro da inganta harkar noma.