1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Bikin Easter cikin tsauraran matakan tsaro

March 30, 2018

Mabiya addinin Kirista a arewa maso gabashin Najeriya sun shiga sahu ‘yan uwan su na fadin duniya wajen yin bukukuwar Easter inda ake gudanar da bukukuwan cikin tsauraran matakan tsaro.

Nigeria Weihnachten - Peter Eshioke Egielewa beim Gottesdienst in Lagos
Hoto: DW/G. Hilse

Dubun-dubatar mabiya addinin kirista a jihohin arewa maso gabashin Najeriya sun yi fitar dango zuwa majami'u cikin ko dai sabbin kaya ko kuma wankakku domin yin addu'o' da wakokin yabo a wani bangare na bukukuwan Easter na bana.  Ga misali a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno an samu fitar jama'a zuwa majami'u domin wannan bikin na Easter sabanin shekarun baya da mutane suka noke a gidajen su saboda fargabar hare-hare da ake alakantawa da Boko Haram ya haifar a shiyar.

An gudanar da addu'o'i da wakoki a majami'u a wani bangare na bikin Easter na banaHoto: AP

Sauran yankuna da ake da zaman lafiya ma kamar kudancin Borno mabiya addinin kirista sun a gudanar bukukuwan cikin kwanciyar hankali ba kamar shekarun baya ba. A ziyara da wakilin DW ya kai daya daga cikin majami'u da ke Maiduguri ya tarar da mabiya addinin kirista suna addu'o'i da wakoki na yabo.Haka labarin yake a sauran jhohin Adamawa da Bauchi da Gombe da Taraba da Yobe inda nan ma ake bukukuwan cikin kwanciyar hankali.

An sanya tsauraran matakan tsaro a hanyoyin da majami'u suke don tsare lafyar masu ibadaHoto: Katrin Gänsler

Sai dai ana bukukuwan ne cikin tsauraran matakan tsaro inda jami'an tsaro na gwamnati da matasa da ke kula da tsaro a coci-coci da ke kafa shingen suna bincika duk mai shiga tare da amfani da na'urori don tabbatar da ba a shiga da wani abu da zai cutar da jama'a ba. Mabiya addinin kirista sun samu damar yin tafiye-tafiye zuwa garuruwa da kauyukan su na asali domin alamta wannan rana da kuma yin bukin cikin ‘yan uwa da abokan arziki don kara dankon zumunci.