1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken kwangila ko bibiyar 'yan adawa?

October 23, 2025

A yayin da ake kara matsawa zuwa ga zabukan Tarayyar Najeriya cikin yanayi maras tabbas, majalisar wakilai ta ce tana shirin sake kaddamar da bincike kan wata kwangilar samar da tsaron babban birnin kasar Abuja.

Najeriya | Bincike | Kwangila | Tsaro | Abuja | Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban kasa a Najeriya Goodluck JonathanHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Kimanin dalar Amurka miliyan 460 ne dai, ake fadin sun bi ruwa a kwangilar da ke neman rikidewa ya zuwa kafa ta siyasa. Ya zuwa yanzun dai ana nuna alamun raba gari, a tsakanin magoya bayan tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da ya bayar da kwangilar shekaru 15 can baya da gwamnatin APC da ke fadin ana bukatar sake lale.

Ina makomar kwangilar ta sama da shekaru 15?

Duk da cewa dai tun kusan shekaru 15 aka kai bayar da kwangilar kafa wasu kyamarori na bincike da samar da tsaron babban birnin Tarayyar Najeriyar da ke Abuja, kokarin bincike kan aikin dai yanzu haka na neman rikidewa ya zuwa bakar siyasa a kasar. A shekara ta 2010 ne dai tsohuwar gwamnatin Jonathan ta bayar da kwangilar kyamrorin kusan 2000, a wani mataki na tsare birnin da ke dada fuskantar rashin tsaro da ta'addar Boko Haram.

Babandede ya yi tir da cin hanci a Najeriya

03:57

This browser does not support the video element.

An dai kare ba tare da kwaliyya ta biya kudin sabulu ba, to sai dai kuma tuni yunkurin sake kaddamar da binciken ke janyo kace-nace cikin fagen siyasar Najeriyar. Masu adawa dai na fadin kokarin sake kaddamar da binciken na da launi na siyasa, maimakon tabbatar da gaskiyar abun da ya faru. To sai dai kuma wajen APC, Jonathan din bai wuci magen lamin da bai zama barazana cikin gidan na tsintsiya ba.

Kada gangar siyasa

Daga dukkan alamu dai, ana ta kara daurin damara cikin gwagwarmaya ta mallakar ruhin Najeriyar a nan gaba. Kuma ko ya zuwa ina bincike na masu dokar ke shirin zuwa da kamar wuya ya sauya tsari na kasar yanzu haka, a tunanin Dakta Faruk BB Faruk da ke sharhi cikin siyasa ta kasar. Najeriyar dai na kara matsawa zuwa gaba, cikin bakar siyasar da ke da tasiri ga rayuwa da kila ma makomar miliyoyin 'yan kasar anan gaba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani