Fatan 'yan Najeriya a sabuwar shekarar 2022
January 1, 2022
Najeriyar da ta share dari na shekaru cikin batu na hadin kai dai na tangal-tangal tun da safiya ta sake sabuwar darin cikin tafiyar mai tsidau da kaya. Duk da cewar sabuwar awaren na dada kamari ne a lokaci na neman mulki a kasar, ra'ayi cikin kasar dai yana rabe bisa sahihancin neman warewar da ta faro jim kadan bayan zabe na 2015. Abdul Aziz Sulaiman dai na zaman kakaki na gamin gambiza ta matasan arewacin kasar da ke fadin warewar ce alheri ga makomar yankin nasu. ''Araba kowa ya kama hanya ta garinsu ko kuma a fake da rabawar da nufin cika buri na siyasa dai, in har arewacin tarrayar Najeriyar na fadin kowa ya tafi gida, ga masu fafutukar Biafran dai rashin adalci na kasar ne ke dada kai su zuwa bango a fadar Nnameker Ejiofor da ke zaman daya a cikin lauyoyin jagoran Biafran Nmandi Kanu.. ''Abun bakin ciki ne ace har yanzu a karni na 21, Najeriya na makance ga adalci, har yanzu na makance ga yakamata, har yanzu na makance ga amintaccen tsari na kasa da kasa. IPOB dai kungiya ce mai neman zama na lafiya, dake rajin yanci na cin gashin kai, da ke neman 'yancin cire kansu daga sarkar son zuciyar da ta mamaye wannan gwamnati. Abun da kawai suke nema ke nan adalci.”Zabukan da ke karatowar dai daga dukkan alamu na zaman zakaran gwajin dafi na makomar tarrayar Najeriya, kasa mafi girma a nahiyar Afrika ga batun yawan al'umma da tattali na arziki. 'Yan Najeriyar dai na fatan a wannan sabuwar shekara ta 2022 za a samu sauyi na tafiyar al'amura cikin kwanciyar hankali domin samun ci gaba mai dorewa.