1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta kafa tutocinta a Jihar Niger

Uwais Abubakar Idris AH
April 27, 2021

A  ci gaba da kara tabarbarewar yanayin tsaro a Najeriya musamman a yankin arewa maso yammacin kasar gwamnan jihar Niger ya tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram ta kafa sansaninta a Niger.

Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

Bullar kungiyar a kararmar hukumar Shiroro ta Jihar Niger dai ya ta da hankali sosai saboda yadda jihar ke shan fama da kai hare-haren da aka yi ta zargin lamarin ya wuce na garkuwa da jama’a, zargin da a yanzu gwamnan jihar Abubakar Sani Bello a fusace ya bayyana cewa bai kamata a kyale mayakan Boko Haram kafa sansanin a kusa da fadar gwamnatin Najeriya.

Mr Bulus Etsu na cikin mutanen da wadannan hare-hare ya shafa ya bayyana mummunan halin da suka shiga. Ta dai kai ga majalisar dattawan Najeriya gudanar da zama na musamman a kan rahoton bullar 'ya'yan kungiyar Ahlu Sunna Li Da’awati Waljihad a jihar ta Niger, inda bayan muhawara suka bukaci a dauki mataki saboda abin da suka kira barazanar rashin tsaro da ta taso Najeriya daga sassa dabam-dabam na kasar.

Kasancewar kusanci da ma makwabtaka tsakanin Abuja da Jihar Niger inda aka samu bullar wannan kungiya dai ya sanya kwararru a fannin tsaro irin su Dr Yahuza Getso, bayyana barazanar da ke fuskantar babban birnin na Najeriya da ke zama mai cikakken tsaro.

Najeriyar dai na cikin mawuyacin hali na rashin tsaro kama daga Maiduguri zuwa Zamfara da Kaduna da ma jihohin Imo da Anambra duka kanwar ja ce ta neman mafita daga matsalar ta rashin tsaro da a bayyane ta zamewa Najeriyar dan hakin da ka raina.