1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Mayakan Boko Haram sun halaka sojoji

Ramatu Garba Baba
June 8, 2020

Mayakan Boko Haram sun halaka sojojin Najeriyan shida a yayin wani hari da suka kai kan sansaninsu da ke jihar Borno a yankin Arewa Maso Gabashin kasar da kungiyar ke ci gaba da yada manufarta.

Niger Symbolbild Armee
Hoto: AFP/S. Ag Anar

Sojoji shida ne suka kwanta dama, a yayin wani gumurzu a tsakaninsu da mayakan Boko Haram a jihar Borno. Masu gwagwarmaya da makaman sun kai harin na bazata a sansanin sojin da ke yankin Arewa Maso Gabashin kasar. Daya daga cikin jami'an sojin, ya ce sun yi rashin nasara kan mayakan a fafatawar da aka kwashi fiye da sa'o'i biyu ana yi.


Akwai sojoji sama da arba'in da ba a ji duriyarsu ba tun bayan artabun, amma ana ganin sun tsere ne a yayin barin wutar inji wani abokin aikinsu. A dai daren ranar Asabar aka kai harin, a yankin da ayyukan masu tayar da kayar bayan, suka yi sanadiyyar dubban rayuka da tilasta ma mutane fiye da miliyan daya rasa matsuguni.