Najeriya: Buhari zai yi takara a 2019
April 12, 2018Talla
Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da wannan aniya tasa ce a taron jam'iyyarsa ta APC da ya gudana a ranar tara ga wannan wata na Afrilun da muke ciki a garin Abuja. Wannan dai ya kawo karshen kila-wa-kala da aka jima ana yi kan batun sake tsayawar ta Buharin ta la'akari da shekarunsa. Kundin tsarin mulkin Najeriya dai ya halatta yin wa'adin mulki na shekaru hurhudu sau biyu, sai dai bai kayyade yawan shekarun 'yan takarar neman shugabancin kasar ba, wanda ke nufin duk da kasancewa yana da shekaru 75 a yanzu, Shugaba Muhammadu Buhari na na da damar sake tsayawa takarar.