1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira ga masu zanga-zanga a Najeriya

October 22, 2020

Yayin da aka share tsawon makonni biyu ana zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali a Najeriya, majalisar tsaron kasar ta bukaci matasan kasar da su ajiye makaman tayar da hankalin.

Nigeria Abuja | Prsident Muhammadu Buhari ernennt Ibrahim Gambari zum Stabschef
Taron majalisar tsaron Najeriya, ya bukaci matsan da ke zanga-zanga su ajiye makamaiHoto: Reuters/Nigeria Presidency

Majalisar tsaron Najeriyar dai ta yi wannan kira ga matasan ne, yayin taronsu da suka gudanar a Abuja fadar gwamnatin kasar. Wannan ne dai karo na farko da daukacin hafsoshin tsaron kasar da ragowar shugabannin tsaron ke ganawa, tun bayan tashin rikicin makonni biyu baya. Kuma babban taron majalisar tsaron a karkashi na shugaban kasar, bai yi wata-wata ba wajen nunin hanyar da gwamnatin kasar take shirin ta bi da nufin warware matsalar da ke neman tashi daga kai karshen 'yan sandan SARS ya zuwa kone dukiyoyin jama'a cikin gari.

Karin Bayani:  Kwaskwarima ga tsarin 'yan sandan Najeriya

Bayan kammala taron dai, mashawarcin tsaron kasar Janar Babagana Monguno  ya ce shugaban kasar yana shirin sanar da jeri na matakan kai karshen matsalar a kankanin lokaci. Mongunon da ya nemi matasa ajiye makamai nan take dai, ya ce gwamnatin kasar ba ta shirin kyale abubuwa su lalace a cikin sunan 'yanci.
Balla a kokari na na'isa ko kuma neman 'yanci na walwala dai, ya zuwa yanzu dai rikicin na tashi da lafawa a birane dabam-dabam na kudanci na kasar. Ana saran wani sabon jawabi a bangare na shugaban kasar Muhammadu Buhari ya zuwa  safiyar Jumma'a mai zuwa, a kokari na kwantar da hankula na 'yan kasar da ke  dada tashi. Akwai dai tsoron rikidewar rikicin ya zuwa ga batun addini da kabilanci, bayan da wasu a cikin kungiyoyin kabilar Yarabawa suka fara zargi na kokari na lalata dukiya da sunan zanga-zangar daga bangaren matasan kabilar Igbo a birnin Lagas, a yayin kuma da kungiyar Ohaneze ta 'yan kabilar ta Igbo ke fadin an taka an kuma zubar musu a Abuja.

Matasa na ci gaba da zanga-zanga a NajeriyaHoto: Pius Utomi EkpeiAFP/Getty Images

Karin Bayani:  Gwamnati ta yi biris da kisan masu zanga-zanga

Hon Sha'aban Sharada na zaman shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilan Tarayyar Najeriya, kuma ya ce ana bkatar bude ido a cikin rikicin da ke zaman irinsa na farko ga gwamnatin kasar 'yar sauyi. Da kyar da gumin goshi ne dai Najeriyar ta kare yakin basasa shekaru 50 baya, sakamakon rikici na siyasar da ya rikide ya zuwa na kabilanci a tsakanin sassan arewacin kasar da kudancinsa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani