Najeriya: Bukatar fahimtar juna a tsakanin musulmi
April 24, 2019Wannan kokari na samun fahimtar juna a tsakanin mabiya darikun addinin musulunci a Najeriyar, ya taso ne saboda yawaitar furta kalamai na tunzuri ko batanci da sunan addini, lamarin da ke zama matsala ta cikin gida. Cibiyar daidaita mabiya addinan Musulunci da Krista da ke Kaduna wadda ta shirya taron, ta bayyana muhimmancin hadin kai a tsakanin mabiya darikun Izala, Darika da kuma Shi’a domin dorewar zaman lumana da fahimtar juna.
Sheikh Tijjani Bala Kalarawi na daya daga cikin malaman da suka halarci taron ya jaddada bukatar zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai musamman a tsakanin musulmi kasancewar kowace darika mutum ya ke dukkaninsu sun yi Imani da kalmar Shahada.
Shi ma Dr Ishaq Yunus na kungiyar Izala yace haduwa da tattaunawa a tsakanin juna lamari ne da zai karfafa fahimtar a tsakanin juna. Mahalarta taron sun amince cewa samun fahimtar juna a tsakanin mabiya addinin musulunci zai taimaka wajen dinke baraka da kyautata muamala da fahimtar juna musamman a tsakanin su a dai lokacin da ake fuskantar watan azumin Ramadan da ake samun karuwar wa’azi na musulunci a kasar.