1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kiran jama'a na a girka 'yan sanda na jihohi

January 17, 2024

A yayin da ake cigaba da fuskantar ta‘azzaar rashin tsaro a Najeriya yanzu haka ana samun karuwar kiraye-kirayen kafa rundunar 'yan sanda na jihohi da nufin tunkarar matsalar.

Hoto: next24online/NurPhoto/picture alliance

 Tuni dai jihohi da yawa suka kai ga kafa rundunar 'yan sa kai da nuifn tunkarar dillallan zubar jinin da ke ta kara nuna alamun karfi da kila ma wucewa da sani na jami'an tsaron kasar 'yan gado.To sai dai kuma ana kallon karuwa ta bukatar zartarwa ya zuwa kafa 'yan sanda na jihohin a cikin neman tunkarar matsalar da ke zaman ruwan dare gama duniyar kasar a halin yanzu. Kungiyoyi cikin kasar dabam- dabam walau Afenifere masu kokari na kare muradin Yarabawa ko kuma Middle Belt da ke batun tsakiyar Najeriya dai.

Kiraye-kirayen jama'a na kafar rundunar 'yan sandar jiha

Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

 Senator Victor na  zaman daya a cikin dattatwan yankin tsakiyar Najeriyar da ke ji har a kwakwalwa cikin batun rashin tsaron. Batun 'yan sandan na jihohi dai na zaman daya cikin batutuwan da suka dauki hankali  a Najeriya tun daga farko. Kuma an yi ta zargin masu siyasar farkon da amfani da 'yan sandan cikin cin zarafin abokai na adawa ta siyasar daurin.

Sai an canza kudin tsarin mulki ko da za a iya daukar 'yan sandar jihohi

Hoto: Olamikan Gbemiga/AP Photo/picture alliance

To sai dai kuma  a fadar Mohammed Abdulkadir  Indabawa da ke zaman wani tsohon kwamishinan 'yan sanda a kasar, lokaci yayi na yan sandan  na jihohi, sakamako gazawar na tarrayar na sauke nauyin na tsaro cikin kasar. Ana bukatar sauyin kundin tsarin mulki na kasar kafin iya kaiwa ga tabbatar da 'yan sanda cikin jihohi na kasar, a fadar Kabiru Adamu da ke zaman kwararre bisa harkar ta tsaro.'Ya zuwa yanzu dai kasar na da jami'an 'yan sanda 370,000 cikin kasar da ke da bukatar karin 'yan sanda kusan 200,000. Majalisar Dinke Duniya dai ta ce ana bukatar akalla dan sanda guda daya domin ba da kariyar mutane 450 maimakon 600 da ke a karkashin kowanne dan sanda cikin kasar a halin yanzu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani