Najeriya: Kalubalen sabbin dokokin aikin hajjin bana
April 30, 2025
Gargadin na zuwa ne a dai dai lokacin da masu ruwa da tsaki suka bayyana samun shawo kan dukkanin kalubalen da ake fuskanta a yanzu domin aikin hajjin na wannan shekara da ke cike da kalubale.
Gagarumin taro ne a kan aikin hajiin na bana a kokari na shaidawa juna gaskiya a kan halin da ake ciki a yanzu, inda baya ga batun shirye-shiryen da ake yi, masu ruwa da tsaki suka tabo batutuwa da suka shafi sabbin tsaren-tsaren aikin hajjin na bana da sabbin dubarun da aka tsara don samun dorewar aikin hajji cikin sauki ga maniyata. Hajiya Fatima Usara mataimakiyar darakta a hukumar ta shaida min sauyi da aka samu tare da gargadi ga masu aniyar kutse ga aikin.
‘'A bana dai hukumomin Saudiyya suna jan kunne maniyyata a kan cewa su tabbata sun samu takardun visa na kwarai ba na boge ba kafin su shiga kasar Saudi Arabiya. Idan aka kama wanda ya shiga baya da takaradar izini abinda ya kamata za'a ci shi tarara riyal dubu 20 zuwa dubu 100 kuma za'a tasa keyarsa zuwa Najeriya tare da haramta mashi shiga kasar Saudiyya na tsawon shekaru 10''.
Duk da cewa an tsaida ranar 9 ga watan Mayu domin fara jigilar maniyatan Najeriya fiye da dubu 40, an fuskanci kalubale mai yawa a daukacin tsarin na bana yake cike da sauye-sauye. Maniyyata da ke tafiya ta jirgin yawo sun kaiga daga yar yatsa, ko wane hali ake ciki a yanzu? Abubakar Sideeq Muhammad shi ne shugaban kamfanin jirgin yawo na Comrel da ke Najeriyar.
‘'Da akwai matsala amma an samu mafita a yanzu tare da wani kamfani na Rawaf wanda zai samar da tantin da maniyyata za su zauna bisa ga tanti na daya da na biyu, wannan shi ne taron da muka yi kuma an samu mafita an ma san nawa za'a bi an kuma ce a fara biya''
Hukumar aikin hajjin Najeriya ta duba bukatar kyautata dubarar nan ta adashin gata ga maniyyata, ta yadda za'a samu tsari mai dorewa na biyan kudin aikin hajji cikin sauki da rahusa. Farfesa Muhammad Nasirudeen Mai turare shi ne shugaban cibiyar koyar da aikin hajji ta Najeriya.
To sai dai ga kwararru a fanin hada-hadar kudi irin su Dr Mansur Muktar tsohon mataimakin shugaban bankin bunkasa anddinin Islama na mai bayyana abinda ya kamata a yi.
Aikin Hajji dai na ci gaba da samun sauye-sauye da ci gaba abinda ya sanda zama wajibi ga Najeriya ta bi sahu wannan sauyi don kaucewa barinta a baya.