Kashe-Kashe a Najeriya: CAN ta magantu
August 7, 2020Reverend Yakubu Pham dai shi ne shugaban hadaddiyar kungiyar Kiristocin Arewacin Najeriyar wato Northern CAN, kuma yayin ziyarar tasa a Kaduna da zai kwashe tsawon kwanaki biyu, zai tattauna hanyoyin kawo karshen zubar da jinni da sauran tashe-tashen hankula da ke haifar da matsaloli dabam-dabam a tsakanin mabambanta addinai da kabilu a yankin na kudancin Kaduna.
Ziyarar tasa dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka sake samun wani hari daya lakume rayukan mutane sama da 28 a cikin kwanaki biyu kacal.
Shugaban na CAN yankin arewacin Najeriya, ya kara da cewa lallai akwai bukatar yin yafiya da kuma bai wa al'ummar yankin damar tatattauna dukkanin abubuwan da ke damunsu. Wadannan sababbin rigingimun da hare-haren da ke faruwa, na zuwa ne yayin da gwamnatin jjhar Kadunan ta sanya dokatr ta-baci a wasu yankuna da ake samun tashe-tashen hankula.
Shugaban kiristocin Reverend Pham ya jaddada muhinmancin kwantar da hankalin daukacin al'ummar yankin a wannan lokaci, da kuma bukatar ganin gwamnati ta kara yawan jami'an tsaro tare da janyo hankalin kungiyar CAN ta jihar Kaduna kan lura da irin kalaman da take furtawa domin kawo zaman lafiya da samun kyakkyawar fahimta tsakanin alummar yankin.
Wadannan rigingimu wadanda suka samo asali tun sama da shekaru 40 da suka gabata, na ci gaba da janyo rarrabuwar kawuwanan al'ummar yankin. Shi kuwa a nasa bangaren, Sheick Halliru Maraya yayin wani taron zaman lafiya da aka kammala cewa ya yi akwai bukatar samun hadin kai tsakanin malaman addinai domin magannce matsalolin. Idan dai ba a mantaba, cikin wannan makon ne gwamnatin jihar Kaduna, ta bayyana cewa kimanin naira biliyan 16 ne ta kashe cikin shekaru biyar din da suka gabata wajan magance matsalar tsaro.