1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barkewar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya

July 5, 2018

Kasa da 'yan awoyi da ayyana kafa bangare cikin jam’iyyar APC mai Mulki a Tarayyar Najeriya, hankula sun tashi a tsakanin manyan 'yan jam’iyyar da suke kallon babbar barazana ga jam’iyyar da ke fatan ci gaba da mulki.

Karikatur: Nigeria APC Streit
Hoto: DW / Abdulkareem Baba Aminu

A can a hedikwatar jam’iyyar na kasa dai babu masakar tsinke sakamakon wani taro na majalisar zartarwa ta kasar da ke gudana  da kuma  daga dukkan alamu ke nazarin mafitar sabon rikicin jam’iyyar  mai mulki, a yayin kuma da a cikin ita kanta fadar shugaban kasar wasu manyan gwamnonin APC na Jihohin Jigawa da Zamfara da kuma Kebbi ke kai kawo a tsakanin offishi na shugaban kasar ya zuwa na babban jami’in tafiyarwa na gwamnatin a wani abun da ke zaman alamun tashin hankali cikin jam’iyyar.
Alamu na zubar yawu a tsakani na masu tsintsiyar dai na kara karuwa tare da ayyana ballewar 'yan APC ta masu neman sauyi ga irin dauri na tsintsiyar.

Tuni dai dama aka rika hasashen kwabewar lamura a cikin jam’iyyar yayin babban taro na kasa makonni biyu da suka gabata, to sai dai kuma ayyana ballewar ta ranar Laraba dai na zaman aiken sako a cikin APC da ke fatan kaiwa ya zuwa babban zabe a cikin dauri guda daya. Inginiya Buba Galadima dai na zaman daya daga cikin masu neman sauyin, Kuma a fadarsa kokari na kwatar hakkin talaka na zaman babbar hujja ta wannan mataki na su.

Bangarewa zuwa gida-gida dai na zaman salon da ya kai Jam’iyyar PDP zuwa ga adawa, kuma daga dukkan alamu shi yake shirin sake dora ta gadon mulki sakamakon sabon rikicin cikin gida na masu tsintsiyar. Duk da cewar dai sabo na shugabancin APC ya kaddamar da tattaunawa a tsakanin sassan da ke fadin an bata,  zai wahalar gaske a iya kaiwa ga tabbatar da samun sulhun da ake bukata kasa da wattani da sake komawa filin daga na zabe.


An dai rabakan 'yan  jam’iyyar a tsakanin gwamnonin da ke jan ragamar harkokin APC da goya baya na shugaban kasar da kuma 'yan majalisun Tarrayar da ke tsakanin tawaye da ganin karshen tasirinsu cikin harkokin siyasar ta Najeriya. A jihohin kasar da daman gaske dai tuni an tsaida masu takarar da zasu maye gurbin dattawa da wakilan da ke jan ragamar ta adawar cikin gidan jam’iyyar. To sai dai kuma duk da hakan a fadar Ibrahim masari da ke zaman babban jami’in kula da walwala na kasa a jam'iyyar ta APC, har yanzu  ba a makara ba a kokari na kaiwa ga dinke tsintsiyar wuri daya.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani