1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ci gaba da aikin ceto bayan hadarin kwale-kwale

Abdullahi Tanko Bala
June 14, 2023

Hukumomi a Najeriya suna ci gaba da aikin ceto bayan hadarin jirgin kwale-kwale da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 100 a Jihar Kwara da ke arewa maso tsakiyar Najeriya

Hadarin jirgin ruwa a Najeriya
Hoto: AP/picture alliance

Mutane fiye da 100 suka rasu a arewa maso tsakiya Najeriya bayan da kwale-kwalen da suke ciki dauke da iyalai da ke dawowa daga bikin aure ya nutse a ruwa a cewar 'yan sanda.

Har kawo yanzu ba a sami cikakken bayanin musababbin hadrin ba wanda ya auku a jihar Kwara. Sai dai wannan na daga cikin hadari na baya bayan nan na jirgin kwale kwale da ake yawan samu sakamakon daukar mutane fiye da kima da rashin ingancin kwale-kwalen da kuma ambaliyar ruwa da ake samu a lokacin damuna.

Rahotanni daga rundunar 'yan sanda da kuma ofishin gwamnan jihar Kwara sun ce jirgin ya kwaso mutanen da suka je biki ne a makwabciyar jihar Neja a lokacin da ya nutse.